Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta sanya 7 ga Agusta a ranar daurin auren gata

Gwamnatin Kano ta sanya 7 ga Agusta a ranar daurin auren gata

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya ranar Juma’a 7 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar da za a gudanar da daurin auren gata ga ‘yan mata da zawarawa 1,500 daga sassan jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mai Daukar Rahoton Gwamna a Hukumar Hisbah, Bashir Ahmad Muhammad, ya fitar a ranar Asabar, 25 ga Yulin 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa ranar ta yi daidai da 24 ga watan Safar, 1448 bayan Hijira, tare da umartar dukkan ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da bikin cikin nasara.

A cewar sanarwar, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dakta Imam Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayar da wannan umarni, inda ya bukaci ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su gaggauta fara shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da nasarar bikin daurin auren.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments