Attajirin duniya kuma shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX, Elon Musk, ya yi hasashen cewa muhimmanci kuɗi zai ragu matuƙa nan da shekaru 10 masu zuwa, sakamakon ci gaban fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) da mutum-mutumi.
Musk ya bayyana cewa nan da shekarar 2036, AI da mutum-mutumi za su riƙa samar da kayayyaki da ayyuka fiye da yadda mutane za su iya amfani da su, lamarin da zai sa a fara tambayar ko har yanzu akwai buƙatar kuɗi kamar yadda ake amfani da su a yau.
Ya kuma yi hasashen cewa a nan gaba za a iya samar da tsarin da kowa zai riƙa samun kuɗin shiga ba tare da la’akari da irin aikin da yake yi ba.
Bugu da ƙari, Musk ya yi gargadin cewa China na ci gaba da ƙarfafa matsayinta a fannin fasahar AI, kuma na iya zama ƙasa mafi rinjaye a wannan fanni a nan gaba.