Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiFadar shugaban kasa ta mayar wa Atiku martani kan zargin Tinubu

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Atiku martani kan zargin Tinubu

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ƙoƙarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na sake tayar da batun kwacen kadarorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Amurka ba zai amfane shi a siyasa ba.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce sake dawo da zarge-zargen da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 ba zai ƙara wa Atiku wata dama a zaɓen 2027 ba.

Onanuga ya kuma yi zargin cewa Atiku ya kashe Dala miliyan 1.2 wajen ɗaukar hayar wani kamfani a Amurka domin yaɗa korafe-korafe kan Shugaba Tinubu.

A cewarsa, da ace Atiku ɗan ƙasar China ne, da tuni an gurfanar da shi a gaban doka bisa abin da ya kira laifuffukan da ya aikata.

Ya kuma soki Atiku kan ci gaba da neman goyon bayan ƙasashen waje kan batutuwan siyasar cikin gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments