Sunday, October 18, 2026
HomeKasuwanciAmurka ta sanya sabon harajin kashi 12.5 kan kayayyakin da Najeriya ke...

Amurka ta sanya sabon harajin kashi 12.5 kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa

Amurka ta sanya sabon harajin kashi 12.5 cikin 100 kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasar, a wani sabon tsarin kasuwanci da ya shafi ƙasashen da Washington ke zargin ba su da cikakkiyar doka da za ta hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas.

Amurka ta sanya sabon harajin kashi 12.5 cikin 100 kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa ƙasar, a wani sabon tsarin kasuwanci da ya shafi ƙasashen da Washington ke zargin ba su da cikakkiyar doka da za ta hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas.

Ofishin Wakilin Kasuwancin Amurka (USTR) ya ce Najeriya na cikin ƙasashe 60 da aka gudanar da bincike a kansu bisa sashe na 301 na dokar kasuwancin Amurka.

A cewar USTR, ƙasashen da suka riga suka kafa ko suka yi alƙawarin kafa dokar da za ta hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas za su fuskanci harajin kashi 10 cikin 100. Sai dai Najeriya da sauran ƙasashen da ba su da irin wannan tsarin za su biya kashi 12.5 cikin 100.

Hukumar ta ce an fara binciken ƙasashen 60 ne a watan Mayun 2026, bayan an gudanar da shawarwari da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki. Ta ce ta karɓi bayanai sama da 1,600, tare da sauraron shaidu daga mutane sama da 100.

Sabon harajin ya zo ne bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi amfani da sashe na 122 na dokar kasuwanci ta shekarar 1974 wajen sanya wani haraji na wucin gadi kan kayayyakin da ake shigowa da su Amurka.

Sai dai USTR ta ce wasu kayayyaki za su samu rangwame daga sabon harajin, musamman albarkatun ƙasa da hana shigarsu ka iya haifar da ƙarancin kayayyaki ko matsala ga tattalin arzikin Amurka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments