Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDaliban polytechnic 5 sun samu ’yanci bayan shafe makonni 7 a hannun...

Daliban polytechnic 5 sun samu ’yanci bayan shafe makonni 7 a hannun masu garkuwa

Daliban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara, waɗanda aka sace a ranar 3 ga Yuni, 2026, sun samu ’yanci bayan shafe kusan makonni bakwai a hannun masu garkuwa da mutane.

Daliban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara, waɗanda aka sace a ranar 3 ga Yuni, 2026, sun samu ’yanci bayan shafe kusan makonni bakwai a hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun ce jami’an Hukumar DSS ne suka ceto daliban, waɗanda aka sace daga masaukinsu da ke wajen makaranta a yankin Low-cost na garin Kaura Namoda. Wata majiya daga bangaren tsaro ta ce daliban da aka ceto sun haɗa da maza huɗu da mace ɗaya.

Majiyar ta ce an kama ɗaya daga cikin masu garkuwar yayin aikin ceto, yayin da aka kashe sauran waɗanda suka yi yunƙurin tunkarar jami’an tsaron. A cewarta, bayan an saki biyu daga cikin daliban shida da aka sace tun farko, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara wani samame na musamman da ya dogara da bayanan sirri, wanda ya kai ga kubutar da sauran daliban.

Bayan sace daliban, shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda, Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawowar daliban cikin aminci.

Wani dalibin makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya samu damar tserewa, lamarin da ya bar dalibai maza uku da mata uku a hannun masu garkuwar.

Ƙungiyar Concerned Citizens of Kaura Namoda ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin, inda ta zargi wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Bello Dansadiya, da ƙungiyarsa da hannu a wasu hare-hare da sace-sace.

Ƙungiyar ta kuma tunatar da wasu hare-haren baya, ciki har da sace manyan malamai biyu da aka tsare sama da watanni biyu duk da biyan kuɗin fansa. Ta kuma ce an taɓa sace wasu mazauna yankin uku da wani hakimin gari daga gidansa da ke kusa da sansanin sojoji.

A baya, rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace daliban, inda ta ce jami’an tsaro sun ƙara ƙoƙarin ceto su. Rundunar ta ce ɗaya daga cikin daliban ya tsere, yayin da ake ci gaba da neman sauran.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan ɗaya daga cikin daliban ya fita da daddare domin yin fitsari, inda ya bar ƙofar masaukin a buɗe. Daga nan ne wasu ’yan bindiga da ke wucewa suka shiga gidan tare da sace daliban.

Rundunar ’yan sanda ta ce jami’an sashen Violent Crime Response Unit (VCRU), tare da sojojin Operation Fansan Yamma, sun ƙaddamar da wani shiri na haɗin gwiwa domin ceto daliban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments