Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn bai wa ‘yan wasan da suka ci Kofin Duniya kyautar tumatur...

An bai wa ‘yan wasan da suka ci Kofin Duniya kyautar tumatur a matsayin kyauta a garinsu

’Yan wasan ƙasar Sifaniya, Gavi da Fabián Ruiz, sun samu wata kyauta ta musamman daga ’yan garinsu na Los Palacios y Villafranca a wani bikin karrama su.

’Yan wasan ƙasar Sifaniya, Gavi da Fabián Ruiz, sun samu wata kyauta ta musamman daga ’yan garinsu na Los Palacios y Villafranca a wani bikin karrama su.

A yayin bikin, an ba ’yan wasan kyautar tumatur, inda aka auna nauyin tumaturin da aka bai wa kowannensu.

Fabián Ruiz ya samu tumatur mai nauyin kilogram 85, yayin da Gavi ya samu kilogram 68.5, wanda ya kai jimillar kilogram 153.5.

An ce kyautar na daga cikin hanyoyin da al’ummar garin suka nuna alfahari da nasarorin da ’yan wasan suka samu tare da nuna musu godiya bisa wakiltar garinsu da ƙasarsu.

Bikin ya samu halartar jama’a da dama, inda aka karrama ’yan wasan tare da nuna farin ciki kan nasarorin da suka samu a fagen ƙwallon ƙafa.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments