Majalisar Wakilan Najeriya ta sanar da shirin gudanar da cikakken bincike kan dukkan kadarorin da gwamnatoci suka kwato tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Matakin ya biyo bayan damuwar da majalisar ta bayyana kan abin da ta kira rashin gaskiya, ƙarancin bayyana bayanai da gazawar adana sahihan bayanan kadarorin da aka kwato a tsawon shekaru.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, binciken zai mayar da hankali ne kan gano adadin kadarorin da aka kwato, yadda aka gudanar da su, inda suke a halin yanzu, da kuma ko an yi amfani da su bisa tanadin doka.
Majalisar ta ce binciken na da nufin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana wajen kula da kadarorin gwamnati, tare da tabbatar da cewa an sarrafa su yadda ya kamata domin amfanin al’ummar Najeriya.