Rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) ta tabbatar da kashe Abu Salim al-Barnawi, wani fitaccen kwamandan hare-hare na Boko Haram/ISWAP wanda daga baya ya koma jagorantar sashen ɗaukar hotuna da yaɗa farfaganda na ƙungiyar. Rundunar ta ce an kashe shi ne a yayin da sojoji suka dakile wani hari da ‘yan ta’addan suka kai kan wani sansanin soji a yankin Cross Kauwa a ranar 12 ga Yulin 2026.
Sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Soji na Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a Maiduguri ranar 22 ga Yulin 2026, ta ce an kashe Abu Salim tare da wasu mambobin ƙungiyar masu yaɗa farfaganda ta ISWAP, ciki har da Abu Umar Khattab da Abu Khalid Usman.
Rundunar ta kuma tuna cewa a bayan harin, sojoji sun ƙwato kyamarar bidiyo da wasu kayayyaki daga hannun mayaƙan.
A cewar rundunar, bayanan sirri sun nuna cewa Abu Salim ya taɓa jagorantar hare-haren ta’addanci da ake kai wa ƙasar Kamaru kafin daga bisani a mayar da shi sashen yaɗa labarai na ISWAP.
A wannan aiki ne yake ɗaukar hotuna da bidiyoyin hare-haren ƙungiyar, tare da shirya kayan farfaganda domin ɗaukar sababbin mambobi da yaudarar jama’a.
Operation HADIN KAI ta ce ƙungiyar ISWAP ta tilasta kanta amincewa da mutuwarsa ta hanyar fitar da sanarwar rasuwa, abin da rundunar ta bayyana a matsayin wata alama ta irin matsin lambar da ake ci gaba da yi wa ƙungiyar. Haka kuma, ta ce a harin da ya gaza, an kashe wasu fitattun mayaƙa ciki har da wani ɗan ƙasar Siriya da wani kwamanda mai suna Aliyu Zabarmari, yayin da ake ci gaba da neman wani ɗan haya Balarabe da ya ɓace bayan artabun.
Rundunar ta bayyana cewa ci gaba da kai hare-haren da suka dogara da sahihan bayanan sirri na ci gaba da raunana ƙarfin Boko Haram da ISWAP, tare da lalata tsarin jagoranci da na yaɗa farfaganda na ƙungiyoyin.
Ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da farmaki ba dare ba rana domin kawar da ragowar mayaƙan, rusa hanyoyin tallafa musu da tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.