Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen Badagry a Jihar Legas, ta gano wata jami’ar bogi da ake zargin tana aiki daga wani gida mai dakuna uku a yankin Ilado da ke ƙaramar hukumar Olorunda LCDA.
Hukumar ta ce ta ceto dalibai 106 da ake zargin an yaudare su da alkawarin samun gurbin karatu a wata jami’a ta ƙasashen waje.
Bayan tattara bayanan sirri da gudanar da sa ido na kwanaki, jami’an NSCDC sun kai samame tare da kama wanda ake zargi da kafa cibiyar.
Binciken farko ya nuna cewa ana karɓar miliyoyin naira daga hannun waɗanda ake yaudarar su a matsayin kuɗin shiga makaranta, yayin da ake gudanar da tsarin da hukumomi suka ce ya yi kama da damfarar ilimi.
Hukumar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin tare da ɗaukar matakan doka a kansu.