Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiMahaifi ya rasu tare da ƴarsa a wata tsohuwar rijiya da ke...

Mahaifi ya rasu tare da ƴarsa a wata tsohuwar rijiya da ke Kano

Wani mutum mai shekaru 45, Abubakar Abdullahi, da ’yarsa mai shekaru 15, Fiddausi Abubakar, sun rasu bayan sun faɗa cikin wata tsohuwar rijiya da ba a amfani da ita a ƙauyen Yancibi, ƙaramar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACFO Saminu Abdullahi, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa ofishin hukumar da ke Tsanyawa ya samu kiran gaggawa da yammacin ranar Litinin, 21 ga Yulin 2026, bayan samun rahoton cewa mahaifin da ’yarsa sun faɗa cikin rijiyar.

Jami’an kashe gobara sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto, sai dai duhu da wahalar yanayin wurin sun hana su kammala aikin a daren ranar.

Da safiyar Talata ne aka tura ƙarin tawagar ceto daga hedikwatar hukumar.

Daga bisani jami’an sun samu nasarar fitar da su daga rijiyar, amma a same su ba tare da alamun rai ba, kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.

An miƙa gawarwakinsu ga Hakimin ƙauyen Yancibi, Shamsu Sani.

Binciken farko ya nuna cewa Fiddausi ce ta fara faɗawa rijiyar, yayin da mahaifinta ya shiga domin ƙoƙarin ceto ta, amma shi ma ya makale a ciki, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments