Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiICPC ta gano ma’aikatan bogi 908 a ma’aikatun gwamnatin tarayya

ICPC ta gano ma’aikatan bogi 908 a ma’aikatun gwamnatin tarayya

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta bayyana cewa ta gano ma’aikatan bogi 908 a cikin binciken da ta gudanar a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 50.

Shugaban hukumar, Musa Adamu Aliyu (SAN), ya ce binciken ya nuna cewa an biya kusan Naira miliyan 942 a matsayin albashi ga waɗannan ma’aikatan bogi.

A cewarsa, binciken na daga cikin matakan da ICPC ke ɗauka domin gano da kuma dakile zamba a tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

Aliyu ya ƙara da cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ce ta fi yawan ma’aikatan bogi da aka gano a binciken da aka gudanar zuwa yanzu.

Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan doka kan duk wanda aka samu da hannu a badakalar domin kare dukiyar al’umma da tabbatar da gaskiya a tsarin aikin gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments