Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za ta fara rabon Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) a Jihar Osun daga ranar 22 zuwa 28 ga Yulin 2026, gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.
A cewar INEC, rabon katinan zai shafi waɗanda suka yi sabon rajista, suka sauya wurin rajista, suka nemi maye gurbin katin da ya ɓace ko ya lalace, da kuma waɗanda suka sabunta bayanansu.
Hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da rabon katinan a cibiyoyin rajista 332 da ke faɗin jihar daga 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana, ciki har da ranakun Asabar da Lahadi domin bai wa jama’a damar karɓar katunansu cikin sauƙi.
Bayan wannan mataki, INEC za ta ci gaba da rabon katinan a ofisoshinta na ƙananan hukumomi daga 29 ga Yuli zuwa 7 ga Agusta, 2026.
Hukumar ta kuma jaddada cewa mai katin ne kaɗai zai karɓi PVC ɗinsa, tana mai gargadin cewa ba a yarda wani ya karɓi katin wani ba, domin hakan ya saɓa wa dokar zaɓe.