Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Ƙasa (NESREA) ta fara gudanar da bincike kan wani sinadari da ake zargin ya zube a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan wani hatsarin mota da ya haifar da bayyana farin kumfa a wurin.
A cikin wata sanarwa da mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, ta ce tawagar NESREA ta jihar Kaduna ta kai ziyara wurin domin gudanar da binciken farko tare da tattara bayanai.
Binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ta yi hatsari, lamarin da ya jawo zubewar kayayyakin da take ɗauke da su.
Sai dai hukumar ta ce har yanzu ba a tantance irin sinadarin da ya zube ba.
NESREA ta tattara samfurin farin kumfar, ƙasa da kuma ruwan wani rafi da ke kusa da wurin domin gudanar da gwaje-gwaje a dakin bincike, wanda zai taimaka wajen gano ko sinadarin na da haɗari ga lafiyar jama’a da muhalli.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji kusantar ko taɓa kumfar, ruwan rafin da kuma ƙasar da ke kewaye da wurin har sai an kammala binciken tare da fitar da sakamakon gwajin.