Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tikitin Musulmi-Musulmi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya kasancewa babban ƙalubale ga jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.
A cewarsa, ya yi mamakin yadda Shugaba Tinubu ya sake tsayar da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa duk da muhawarar da aka yi kan tsarin tikitin Musulmi-Musulmi a zaɓen 2023.
“Abin ya ba ni mamaki cewa shugaban ƙasa ya sake gabatar da irin wannan tikiti.
Na san shi mutum ne da yake son daidaito,” in ji Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa har yanzu akwai lokaci kafin wa’adin sauya sunayen ‘yan takara ya cika, yana mai cewa Tinubu na da damar yin la’akari da tikitin da zai fi nuna daidaiton ƙasa.
Kwankwaso ya kuma yaba wa abokin takararsa, Peter Obi, inda ya ce ya fahimci cewa Obi ɗan siyasa ne mai kishin ƙasa kuma abin dogaro.
Ya ce shi da Obi suna da ra’ayi iri ɗaya kan hanyoyin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki, ilimi da bunƙasa ababen more rayuwa a Najeriya.