Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamna ya yi ziyarar bazata da safe, ya tarar da ma’aikata da...

Gwamna ya yi ziyarar bazata da safe, ya tarar da ma’aikata da dama ba sa ofis

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar bazata zuwa sakatariyar gwamnatin jihar da safiyar Litinin, inda ya tarar da ofisoshin ma’aikatu da dama babu ma’aikata.

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar bazata zuwa sakatariyar gwamnatin jihar da safiyar Litinin, inda ya tarar da ofisoshin ma’aikatu da dama babu ma’aikata.

A wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an ga gwamnan yana zagayawa daga wannan ma’aikata zuwa wancan, inda ya tarar da ofisoshi da dama a kulle ko babu ma’aikata, sai wasu ’yan saƙo kaɗan.

Ziyarar ta zo ne a wani lokaci da ma’aikatan gwamnati ya kamata su kasance a wuraren aikinsu, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan halartar ma’aikata a ofisoshin gwamnati.

Ana sa ran matakin gwamnan zai haifar da bincike kan halartar ma’aikata da kuma yadda ake gudanar da ayyuka a sakatariyar gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar ba ta bayyana matakin da za ta ɗauka kan ma’aikatan da aka tarar ba a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments