Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroSojoji sun kama ɗan Sudan da wata ‘yar Ghana kan zargin ta’addanci...

Sojoji sun kama ɗan Sudan da wata ‘yar Ghana kan zargin ta’addanci a Borno

Dakarun Sojin Najeriya sun kama wani mutum ɗan ƙasar Sudan da ake zargin yana da alaƙa da ayyukan ta’addanci, tare da wata mata da ta bayyana kanta a matsayin ‘yar ƙasar Ghana, a wani samame da suka gudanar a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta ce ba ta da takardun izinin zama a Najeriya, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan shigowarsu ƙasar da kuma ayyukansu.

Rundunar sojin ta ce kamen na daga cikin ci gaba da farmakin da take kai wa masu aikata laifuka da kuma ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Ana sa ran jami’an tsaro za su ci gaba da bincike domin gano ko mutanen biyu na da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka ko kuma ayyukan ta’addanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments