Wata kotu ta amince da bayar da beli ga Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah ta Ƙasa, Bello Badejo, kan kuɗin beli na Naira biliyan biyu.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi kan Badejo.
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken sharuddan belin ko kuma ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar ba.
Ana sa ran za a samu ƙarin bayanai daga kotu da kuma lauyoyin ɓangarorin da abin ya shafa nan gaba.