Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaFitattun ’yan siyasa da suka fice daga haɗakar ADC gabanin zaɓen 2027

Fitattun ’yan siyasa da suka fice daga haɗakar ADC gabanin zaɓen 2027

Haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, wadda aka kafa domin tunkarar zaɓen 2027, ta fuskanci sauye-sauye yayin da wasu fitattun ‘yan siyasa suka fice daga cikinta suka koma wasu jam’iyyu.

Daga cikin fitattun waɗanda suka bar haɗakar akwai Peter Obi, wanda ya fice a watan Mayun 2026 bayan ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da kuma shari’ar da ta shafi jam’iyyar sun taka rawa a matakin da ya ɗauka.

Hakazalika, Rabiu Musa Kwankwaso ya bar ADC bayan ficewarsa daga NNPP, inda daga bisani ya koma wata jam’iyya tare da ci gaba da harkokinsa na siyasa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, shi ma ya fice daga ADC, yana mai zargin an tafka maguɗi a tsarin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

A jihar Adamawa kuwa, Aisha Dahiru Binani ta sauya sheƙa bayan rahotannin rashin jituwar cikin gida tsakanin magoya bayanta da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Sauran fitattun da aka rawaito sun bar ADC sun haɗa da tsohon Sanata Elisha Abbo, ɗan Majalisar Wakilai Leke Abejide, tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa (Arewa maso Yamma) Salihu Lukman, da kuma Buba Galadima, wanda ake danganta shi da ficewa daga haɗakar.

Ficewar waɗannan jiga-jigan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kansu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments