Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar da dakatar da zamansa a jam’iyyar da kuma haɗakar jam’iyyun adawa, lamarin da ya sake jawo hankali kan yadda yake yawan ficewa daga manyan jam’iyyun siyasa da ya riƙe muƙaman jagoranci a cikinsu.
A wasiƙar da ya aika wa Shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark, Lukman ya dora alhakin matakin da ya ɗauka kan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya zarga da nuna masa ƙiyayya da kuma ƙoƙarin mayar da shi saniyar ware a harkokin jagorancin haɗakar jam’iyyun adawa a Jihar Kaduna.
Ya ce an riƙa yanke muhimman shawarwari ba tare da an saka shi a ciki ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar dakatar da ayyukansa na siyasa maimakon ci gaba da fuskantar abin da ya kira rashin adalci da wulaƙanci.
Salihu Lukman ya shahara a matsayin mai fafutukar dimokuraɗiyya da gyaran tsarin jam’iyyu. Ya kasance cikin jagororin jam’iyyar CPC kafin ta haɗe da wasu jam’iyyu suka kafa APC a shekarar 2013, sannan ya riƙe muƙamin Darakta Janar na Progressive Governors Forum (PGF).
Sai dai rikice-rikicen cikin gida sun sa ya yi murabus daga PGF a shekarar 2022, sannan a shekarar 2023 ya sauka daga muƙaminsa na Mataimakin Shugaban APC na Arewa maso Yamma, kafin daga bisani ya fice daga APC baki ɗaya a 2024, yana mai zargin jam’iyyar da kaucewa manufofinta da kuma raunana dimokuraɗiyyar cikin gida.
Bayan ficewarsa daga APC, Lukman ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa haɗakar jam’iyyun adawa da ta zaɓi ADC a matsayin dandalinta domin tunkarar zaɓen 2027. Sai dai yanzu ya ce irin matsalolin da ya yi wa APC korafi a kansu sun sake bayyana a cikin ADC, ciki har da nuna wariya, mayar da iko hannun wasu tsiraru da kuma karya alƙawuran da aka yi lokacin kafa haɗakar. Magoya bayansa na ganin yana tsaya wa ƙa’ida ne, yayin da masu suka ke cewa yawan ficewarsa daga jam’iyyu na nuna gazawarsa wajen dorewa cikin haɗin siyasa.