Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da sana’ar tura fina-finai a faɗin jihar, a wani mataki da ta ce na da nufin tabbatar da bin doka da kuma kare tarbiyya da ɗabi’un al’umma.
Mukaddashin Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Mujahiddin Aminuddeen, ya bayyana cewa duk wanda aka samu yana ci gaba da gudanar da wannan sana’a bayan wannan umarni zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Ya jaddada cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da aiwatar da umarnin, tare da hukunta duk masu karya dokar ba tare da nuna bambanci ba.
Sanarwar ta fito ne cikin wani saƙon murya da Dr. Mujahiddin Aminuddeen ya aikewa kafafen yaɗa labarai, inda ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na ƙarfafa bin doka da kiyaye kyawawan ɗabi’u a jihar.