Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMu ke da ikon tsara harkar ma su turi ba Hisba ba...

Mu ke da ikon tsara harkar ma su turi ba Hisba ba – Hukumar Tace Fina-finai

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ita ce ke da ikon gindaya ƙa’idoji da sharuɗɗan gudanar da sana’ar masu turi a jihar, ba Hukumar Hisbah ba.

Kakakin Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya bayyana hakan bayan da Hukumar Hisbah ta sanar da haramta sana’ar turi, tana mai zargin cewa ana amfani da ita wajen yaɗa abubuwan batsa tsakanin matasa.

Ya ce bisa doka, Hukumar Tace Fina-finai ce ke da alhakin sa ido da tsara yadda ake gudanar da harkokin fina-finai da masu ‘downloading’ a Kano, don haka duk wani mataki da ya shafi sana’ar yana ƙarƙashin huruminta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments