Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYau Alhamis ita ce 1 ga watan Safar 1448AH

Yau Alhamis ita ce 1 ga watan Safar 1448AH

A yau Alhamis, 16 ga Yulin 2026, ne aka fara watan Safar na shekarar 1448AH, bayan kammala watan Muharram.

A yau Alhamis, 16 ga Yulin 2026, ne aka fara watan Safar na shekarar 1448AH, bayan kammala watan Muharram.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana yau a matsayin ranar farko ta watan Safar, bayan kwamitocin duban wata a faɗin ƙasar nan sun tabbatar da cewa ba a ga jinjirin watan a daren ranar 29 ga Muharram ba.

Sakamakon haka, an cika watan Muharram zuwa kwana 30, inda ranar Laraba ta kasance rana ta ƙarshe ta watan, kafin a fara watan Safar a yau Alhamis.

Watan Safar shi ne wata na biyu a kalandar Musulunci, kuma yana daga cikin watanni goma sha biyu da Musulmai ke amfani da su wajen tsara ibadu da sauran al’amuran addini.

Ana ƙarfafa Musulmai su ci gaba da gudanar da ibadu, addu’o’i da kyawawan ayyuka a wannan sabon wata, domin babu wani ingantaccen dalili a addinin Musulunci da ke nuna cewa watan Safar wata ne na rashin sa’a ko sharri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments