Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiJam’iyyu uku sun gaza miƙa sunayen ’yan takarar shugaban kasa kafin INEC...

Jam’iyyu uku sun gaza miƙa sunayen ’yan takarar shugaban kasa kafin INEC ta rufe shafinta

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta rufe shafinta na karɓar sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na mataimakansu bayan wa’adin da ta ƙayyade ya ƙare da ƙarfe 11:59 na daren Talata. Sai dai rahotanni sun nuna cewa jam’iyyu uku ba su kammala loda sunayen ’yan takararsu ba kafin rufe shafin.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta rufe shafinta na karɓar sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na mataimakansu bayan wa’adin da ta ƙayyade ya ƙare da ƙarfe 11:59 na daren Talata. Sai dai rahotanni sun nuna cewa jam’iyyu uku ba su kammala loda sunayen ’yan takararsu ba kafin rufe shafin.

Wata babbar majiya a INEC ta bayyana cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun haɗa da APGA, ɓangaren PDP mai biyayya ga Nyesom Wike, da kuma ɓangaren LP ƙarƙashin Nenadi Usman. Sai dai ta ce kusan duk sauran jam’iyyun siyasa sun samu nasarar miƙa sunayen ’yan takararsu domin zaɓen 2027.

Tun da farko INEC ta ƙara wa’adin miƙa sunayen ’yan takara da kwanaki uku bayan roƙon jam’iyyun siyasa, tana mai jaddada cewa ba za a sake ƙara wani wa’adi ba. Hukumar ta ce yanzu za ta fara tantance bayanan da aka miƙa bisa tanade-tanaden Dokar Zaɓe da ƙa’idojinta.

Manyan jam’iyyun siyasa kamar APC, ADC da NDC sun samu nasarar loda sunayen ’yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimakansu. Sai dai wasu jam’iyyun sun miƙa sunan ɗan takarar shugaban ƙasa kawai ba tare da na mataimakinsa ba, yayin da har yanzu ake fuskantar ruɗani kan sunayen wasu ’yan takarar majalisun dokoki a wasu jihohi.

A gefe guda kuma, har yanzu ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan matsayin jam’iyyar ADC bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rikicin shugabancinta. Duk da haka, zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, sunayen shugabannin jam’iyyar ƙarƙashin David Mark ne ke ci gaba da bayyana a shafin INEC, yayin da jam’iyyar ta tabbatar da cewa ta riga ta miƙa sunayen Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a matsayin ’yan takararta na shugaban ƙasa da mataimakinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments