The Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da shigar da tsofaffin ma’aikatan gwamnati na jiha da ƙananan hukumomi cikin shirin Social Equity Programme, domin ba su damar samun ingantaccen kulawar lafiya ta hanyar inshorar lafiya.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Jihar Yobe (YSCHMA), Dakta Babagana Tijjani, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar. Ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan hukumar ta gabatar da ƙudirin faɗaɗa inshorar lafiya ga ma’aikatan da suka yi ritaya.
A cewarsa, shirin na da manufar inganta rayuwar masu ritaya ta hanyar tabbatar musu da samun ingantaccen kulawar lafiya cikin sauƙi da arha. Ya bayyana amincewar a matsayin wani babban ci gaba wajen inganta tsarin ɗaukar nauyin kiwon lafiya a jihar.
Dakta Tijjani ya ƙara da cewa hukumar ta fara shirye-shiryen aiwatar da shirin ta hanyar yin rajista cikin gaskiya tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin masu ritaya, hukumomin gwamnati da cibiyoyin lafiya da aka tantance, domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta sun amfana da shirin ba tare da wata matsala ba.
Ya ce wannan mataki ya sake nuna ƙudirin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni na aiwatar da shirye-shiryen jin daɗin al’umma, musamman masu ritaya da sauran masu buƙatar tallafi, tare da ƙarfafa tsarin samar da ingantaccen kiwon lafiya a Jihar Yobe.