Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Alhamis, 16 ga Yulin 2026, a matsayin ranar farko ta watan Safar na shekarar Hijira ta 1448AH.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Wazirin Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, bayan kammala nazarin rahotannin duban jinjirin watan daga sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar sanarwar, Kwamitin Duban Wata na Majalisar Masarautar Sokoto tare da Kwamitin Duban Wata na Ƙasa ba su samu wani sahihin rahoton ganin jinjirin watan Safar ba a yammacin ranar Talata, 14 ga Yulin 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Muharram 1448AH.
Bisa wannan dalili, an bayyana cewa Laraba, 15 ga Yulin 2026, za ta zama ranar cika watan Muharram zuwa kwana 30, kamar yadda koyarwar addinin Musulunci ta tanada idan ba a ga jinjirin sabon wata ba.
Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Safar, tare da yi musu fatan Allah Ya sa watan ya kasance mai albarka, zaman lafiya da ci gaba ga Najeriya da daukacin al’ummar Musulmi.