Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiINEC ta ƙaddamar da sabon shafin rajistar katin zabe ta intanet

INEC ta ƙaddamar da sabon shafin rajistar katin zabe ta intanet

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙaddamar da wani sabon shafin intanet da zai ba ’yan Najeriya damar gudanar da rajistar katin zaɓe (PVC) da sauran ayyukan masu zaɓe ba tare da zuwa ofisoshin hukumar ba.

Hukumar ta bayyana hakan a ranar Talata, tana mai cewa wannan sabon tsari na daga cikin matakan inganta Rajistar Masu Zaɓe (CVR) gabanin zaɓuɓɓukan da ke tafe.

A cewarta, tsarin zai sauƙaƙa wa masu son yin rajista da kuma rage cunkoso a cibiyoyin rajista.

INEC ta ce waɗanda ke son yin rajista karo na farko za su iya buɗe asusu a INEC Self-Service CVR Portal, su tabbatar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN), sannan su cike bayanansu tare da ɗaukar bayanan halittarsu ta hanyar amfani da wayar hannu.

Bayan cike bayanan sirri kamar suna, ranar haihuwa, adireshi, sana’a, matakin ilimi da sauran bayanan da ake buƙata, masu rajista za su zaɓi jihar, ƙaramar hukuma, mazaba da kuma rumfar zaɓen da suke son yin rajista a cikinta.

Hukumar ta ƙara da cewa sabon shafin zai kuma ba masu zaɓe damar sauya rumfar zaɓe, sabunta ko gyara bayanansu, gano wuraren karɓar katin PVC, da kuma neman maye gurbin katin da ya ɓace, aka sace ko ya lalace cikin sauƙi ta hanyar intanet.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments