Majalisar Wakilan Tarayya ta dakatar da ci gaba da aikin kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar kan kafa ’yan sandan jihohi, bayan karɓar sabon kudirin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike mata kan wannan batu.
A zaman Majalisar na ranar Talata, an yi wa sabon kudirin karatu na farko da na biyu, lamarin da ya nuna an fara ɗaukar matakan duba shawarwarin da bangaren zartarwa ya gabatar domin sauya tsarin aikin ’yan sanda a ƙasar.
Bayan kammala karatun kudirin, Majalisar ta tura shi zuwa Kwamitinta kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki domin yin cikakken nazari, tare da tantance dukkan muhimman tanade-tanaden da ke cikinsa kafin a dawo da shi zauren Majalisar.
Wannan mataki na nufin cewa Majalisar za ta mayar da hankali ne kan kudirin da gwamnatin tarayya ta gabatar, maimakon ci gaba da aiki da nata kudirin da aka gabatar tun farko.
Ana sa ran bayan kwamitin ya kammala aikinsa, zai gabatar da rahotonsa ga Majalisar domin ci gaba da muhawara da kuma yanke hukunci kan makomar kudirin kafa ’yan sandan jihohi a Nijeriya.