Sojojin Najeriya sun ceto mutum 15 da aka yi garkuwa da su bayan sun dakile wani harin ’yan ta’adda a ƙauyen Marge da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
An bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta bakin mai bibiyar rikice-rikice a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Ceton ya biyo bayan bayanan sirri da suka nuna cewa wasu ’yan ta’adda masu ɗauke da makamai suna cikin Marge, lamarin da ya sa dakarun rundunar Operation FANSAN YAMMA suka garzaya yankin.
Da isarsu, sojojin sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan. Daga bisani maharan suka tsere zuwa cikin daji da suka gane an fi karfinsu, inda suka bar waɗanda suka sace a baya.
Rundunar sojin ta ce babu wani soja da ya jikkata a yayin aikin, kuma an mayar da dukkan mutane 15 da aka ceto ga iyalansu cikin ƙoshin lafiya.
W