Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamnatin Tarayya ta ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000

Gwamnatin Tarayya ta ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabon kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi.

Sabon tsarin zai fara aiki ne daga jarabawar (SSCE) ta shekarar 2027.

A baya, kuɗin rajistar jarabawar ya kasance N27,500, wanda ke nuna an yi ƙarin kusan kashi 82 cikin ɗari.

Ma’aikatar Ilimi ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan buƙatar da WAEC ta gabatar na sake duba kuɗaɗen gudanar da jarabawa saboda hauhawar farashin gudanar da ayyuka.

Daraktan kula da manyan makarantun sakandare na ma’aikatar, Adeniji Ibrahim, ya bayyana cewa an cimma matsayar ne bayan taron da Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya yi da hukumomin shirya jarabawa a ranar 31 ga Maris, 2026.

A taron ne ministan ya umarci WAEC da NECO su daidaita kuɗin rajistar jarabawar SSCE.

Haka kuma, Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi, Folasade Boriowo, ta tabbatar da amincewar gwamnatin tarayya kan sabon kuɗin, tare da buƙatar a sanar da dukkan masu ruwa da tsaki domin su shirya kafin fara aiwatar da tsarin daga shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments