Wani sabon rahoton shekara-shekara na ƙungiyar World Giving ya nuna cewa Najeriya ce ta zama ƙasa ta farko a duniya wajen bayar da sadaƙa, inda al’ummarta ke ware kusan kashi 2.8% na abin da suke samu domin ayyukan jinƙai da tallafa wa mabukata.
Rahoton ya kuma bayyana cewa nahiyar Afrika ce ke kan gaba wajen bayar da tallafi, inda al’ummarta ke bayar da tsakanin kashi 1.54% zuwa 1.6% na kuɗaɗen shigarsu, fiye da ƙasashen Turai da ke bayar da kusan kashi 0.6%.
A jerin ƙasashen da suka fi bayar da sadaƙa, Masar ce ta zo ta biyu da kashi 2.45%, sai Ghana a matsayi na uku da kashi 2.19%. Kenya ta biyo baya a matsayi na biyar a duniya, yayin da Uganda ta zo ta shida, sannan Malawi ta kammala jerin ƙasashen Afrika shida da suka shiga cikin manyan ƙasashe goma na duniya.