Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu ta  tsare tsohon Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikatan Gwamnati bayan gurfanar da shi...

Kotu ta  tsare tsohon Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikatan Gwamnati bayan gurfanar da shi a gabanta

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya FCT da ke Maitama ta tsare tsohon shugaban Kotun Da’ar Ma’aikatan Gwamnati (CCT), Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume huɗu da suka shafi cin hanci da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya FCT da ke Maitama ta tsare tsohon shugaban Kotun Da’ar Ma’aikatan Gwamnati (CCT), Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume huɗu da suka shafi cin hanci da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar EFCC ta zargi Umar da karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba daga wasu ’yan kwangila lokacin da yake shugabantar CCT. Sai dai ya musanta zarge-zargen, yayin da kotu ta umarci a tsare shi har zuwa ci gaba da shari’ar.

A lokacin da yake shugabantar CCT, Danladi Umar ya jagoranci shari’o’in wasu fitattun jami’an gwamnati da ’yan siyasa, ciki har da tsohon Alƙalin Alƙalan Najeriya Walter Onnoghen, wanda aka same shi da laifin ƙin bayyana kadarori yadda ya kamata, aka tsige shi daga muƙaminsa tare da hana shi riƙe wani muƙamin gwamnati na tsawon shekara 10.

Sauran manyan shari’un da ya jagoranta sun haɗa da ta tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, wanda aka wanke daga tuhume-tuhume 18 na bayyana kadarori ba daidai ba, da kuma shari’ar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda kotun ta yi watsi da ita saboda rashin gamsassun hujjoji.

Haka kuma Umar ya jagoranci shari’ar tsohon Ministan Harkokin Neja Delta Godsday Orubebe, wanda aka fara samu da laifi kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin, da kuma ta marigayi Alƙalin Kotun Koli Sylvester Ngwuta, wadda CCT ta yi watsi da ita saboda rashin bin matakan ladabtarwa na Hukumar NJC kafin gurfanar da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments