An samu zaman ɗar-ɗar da cacar baki a zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya yayin da ’yan majalisa suka yi muhawara kan zargin cewa har yanzu ba a saki kuɗaɗen ayyukan mazabu ga wakilan sassan ƙasar ba.
Lamarin ya fara ne bayan ɗan majalisa mai wakiltar Aba North/Aba South a Jihar Abia, Alex Mascot Ikwechegh, ya gabatar da ƙuduri inda ya buƙaci a gayyaci Bola Ahmed Tinubu zuwa majalisar domin ya yi bayani kan dalilan da suka sa aka jinkirta sakin kuɗaɗen ayyukan mazabu.
Ƙudurin ya samu goyon bayan wasu mambobin majalisar, yayin da wani ɗan majalisa ya ƙara da shawarar a dakatar da zaman majalisar na tsawon mako guda har sai an warware matsalar.
Sai dai ɗan majalisa mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam a Jihar Filato, Yusuf Gagdi, ya yi kakkausar adawa da ƙudurin.
Ya ce babu wata buƙatar gayyatar shugaban ƙasa, domin hukumomin da ke da alhakin aiwatar da ayyukan ne ya kamata su yi bayanin abin da ya jawo tsaikon.
Har ila yau, Gagdi ya yi watsi da shawarar dakatar da zaman majalisar na mako guda, yana mai cewa hakan ba zai magance matsalar ba kuma ba shi da wani dalili mai ƙarfi.
Adawar da ya nuna ta haddasa muhawara mai zafi tsakanin mambobin majalisar, inda ’yan adawa da wasu mambobi suka yi ta musayar kalamai tare da ihu, lamarin da ya rikita zaman na ɗan lokaci.
Domin dawo da doka da oda a zauren majalisar, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya umarci ‘yan majalisar da su kada ƙuri’a domin yanke hukunci kan ƙudurin.