Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiSama da mutane 10,000 sun nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a Nasarawa

Sama da mutane 10,000 sun nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a Nasarawa

Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa sama da mutum 10,000 ne suka nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a makarantun firamare, bayan gwamnatin jihar ta amince da ɗaukar sabbin malamai ƙarƙashin wani shiri na musamman domin ƙarfafa ilimi a yankunan karkara.

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na wata biyu da aka gudanar a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar da ke Lafia.

A cewarsa, ɗaukar malaman na ƙarƙashin Nasarawa Universal Basic Education Board ne, kuma an tsara shirin ne domin rage matsalar ƙarancin malamai da ake fuskanta a makarantun firamare da ke yankunan karkara.

Ya ƙara da cewa duk malamai 1,000 da za a ɗauka za a tura su kai tsaye zuwa makarantun karkara domin inganta koyarwa da kuma bunƙasa ilimin yara a waɗannan yankuna.

Gwamnatin jihar ta ce wannan shiri na daga cikin matakan da take ɗauka wajen ƙarfafa fannin ilimi da tabbatar da cewa ɗalibai a yankunan karkara sun samu isassun malamai masu ƙwarewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments