Majalisar Dattawan Najeriya na shirin gudanar da zama a ranar Talata domin tattauna cece-kuce da suka taso kan ware Naira biliyan 1.3 ga wata hukuma da ake zargin ba ta da halaccin gwamnati mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council a cikin Kasafin Kuɗin shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa batun ya janyo muhawara bayan an gano cewa an sanya sunan wannan hukuma a cikin kasafin kuɗi duk da cewa ana zargin ba ta da tushe a tsarin hukumomin gwamnatin tarayya.
Haka kuma, jaridar Punch ta ruwaito cewa an karɓi wata takardar naɗi ta bogi mai ɗauke da sa hannun jabu na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a Hedikwatar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba tare da cikakken bincike ko tantancewa ba.
Rahoton ya ce hakan ya bai wa Prince Adeniyi Adeyemi Mathew damar samun ofishi a harabar Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja, abin da ya sa wannan hukuma ta ci gaba da bayyana kanta a matsayin halastacciyar hukuma ta gwamnati na fiye da shekara guda.
Ana sa ran zaman Majalisar Dattawa zai mayar da hankali kan yadda aka samu wannan kuskure, tare da duba matakan da za a dauka domin gano masu hannu a lamarin da kuma hana irin haka sake faruwa a nan gaba.