Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHisbah ta cafke matasa 25 kan zargin aikata badala a Kebbi

Hisbah ta cafke matasa 25 kan zargin aikata badala a Kebbi

Hukumar Hisbah da ke Argungu a Jihar Kebbi ta kama wasu matasa 25 da ake zargi da aikata ayyukan da suka saɓa wa dokokin shari’a a wasu dakunan otal da ke yankin.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri kan wasu ayyuka da ake zargin ana gudanarwa a wasu wuraren kwanan baƙi a garin Argungu.

A cewar hukumar, mutanen da aka kama sun haɗa da maza da mata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tantance zarge-zargen da ake yi musu kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa tanadin doka.

Hisbah ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da duk wani abu da ta bayyana a matsayin saɓawa koyarwar addini da dokokin shari’a, tare da kira ga al’umma su ba ta haɗin kai wajen kare kyawawan ɗabi’u.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa za ta ci gaba da kai samame a wuraren da ake zargin ana aikata irin waɗannan laifuffuka domin tabbatar da bin doka da oda a faɗin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments