Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kashe kimanin Naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗen gwamnati da ya ce ba sa cikin kasafin kuɗin ƙasa.
Atiku ya yi wannan zargi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce sabon rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya nuna akwai kuɗaɗen gwamnati da aka kashe ba tare da cikakken bayani kan yadda aka sarrafa su ba.
A cewarsa, rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a ranar 1 ga Yulin 2026 ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta gaza yin cikakken bayani kan wasu kuɗaɗen gwamnati da darajarsu ta kai kusan kashi biyu cikin ɗari na jimillar tattalin arzikin cikin gida (GDP) na Najeriya.
Atiku ya bayyana cewa irin wannan lamari na buƙatar cikakken bayani da bayyana gaskiya domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen al’umma.
Sai dai gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan zargi a lokacin haɗa wannan rahoto.