Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHoton AI na Oluremi Tinubu tana soya kosai ya jawo ce-ce-ku-ce

Hoton AI na Oluremi Tinubu tana soya kosai ya jawo ce-ce-ku-ce

An yi ta suka ga Cibiyar Yaɗa Labaran Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan ta wallafa wani hoto da aka ƙirƙira ta amfani da kirkirarriyar fasahar AI, wanda ya nuna Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana soyawa tare da sayar da ƙosai.

An yi ta suka ga Cibiyar Yaɗa Labaran Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan ta wallafa wani hoto da aka ƙirƙira ta amfani da kirkirarriyar fasahar AI, wanda ya nuna Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana soyawa tare da sayar da ƙosai.

Hoton, wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta na fadar shugaban ƙasa a ranar Juma’a, ya nuna ta sanye da atamfa mai rubutun “Iya Alakara, fueling the nation with love.”

An wallafa hoton ne bayan Uwargidan Shugaban Ƙasa ta bayyana a wata hira cewa sana’o’i irin su soya ƙosai, gasa masara da yin ƙuli-ƙuli ba sa buƙatar jari mai yawa. Ta ce gwamnatin tarayya na tallafa wa irin waɗannan sana’o’i ta hanyar ba da tallafi, ba rance ba, domin inganta rayuwar al’umma.

Sai dai hoton ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafin X, inda masu amfani da dama suka soki matakin wallafa shi.

Wani mai amfani da shafin ya ce hoton abin takaici ne kuma cin mutunci ga ’yan Najeriya. Wani kuma ya zargi gwamnati da yin ba’a ga talakawa a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki da matsalar tsaro.

Wasu kuwa sun ce hoton ba ya taimaka wa gwamnatin Tinubu, suna mai cewa ba kowa ne zai iya dogaro da sana’ar ƙosai ko ƙuli-ƙuli ba. Haka kuma, wasu sun yi zargin cewa hoton ya karkatar da hankali daga muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma.

Lamarin ya biyo bayan kalaman Oluremi Tinubu da suka jawo mabambantan ra’ayoyi, inda wasu suka ce kalaman ba su dace da halin ƙuncin tattalin arzikin da ake ciki ba, yayin da wasu suka kare ta, suna cewa tana ƙarfafa mutane su rungumi ƙananan sana’o’in da ba sa buƙatar jari mai yawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments