Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ta bayyana cewa yunwa ta kai wani mummunan mataki da ba a taɓa gani ba cikin kusan shekaru goma a Arewacin Najeriya, inda fiye da mutum miliyan 17 ke fuskantar matsananciyar ƙarancin abinci a jihohi tara na yankin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce sabon bincike ya nuna adadin mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa ya ƙaru da kusan miliyan biyu idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a baya, sakamakon ci gaba da rikice-rikicen tsaro da kuma rage tallafin jin ƙai.
WFP ta bayyana cewa hare-haren ƴan ta’adda sun tarwatsa al’umma, sun hana manoma komawa gonakinsu, tare da kawo cikas ga isar da agajin jin ƙai ga mabukata.
Hukumar ta ce matsalar na ƙara ta’azzara a lokacin damina, lokacin da iyalai ke ƙare ajiyar abincinsu kafin lokacin girbi.
A cewar WFP, Jihar Borno ce ta fi fuskantar matsalar, inda fiye da mutum miliyan uku ke fama da matsanancin rashin abinci, ciki har da sama da mutum 750,000 da ke cikin matsanancin hali na yunwa.
Daraktan WFP na yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, Kinday Samba, ya ce idan mutane suka rasa hanyar samun abinci tare da barin muhallansu, hakan na ƙara haddasa rashin tsaro da rashin zaman lafiya, yayin da rikici ke tilasta wa mutane barin gonakinsu.