Sabon Jagoran Koli na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa ba zai halarci jana’izar mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei ba, saboda dalilan tsaro.
Rahotanni sun ce Mojtaba ya yanke wannan hukunci ne bisa shawarar jami’an tsaro, saboda fargabar yiwuwar kai masa hari yayin bukukuwan jana’izar da ake sa ran miliyoyin mutane za su halarta.
An shirya gudanar da jana’izar marigayi Ali Khamenei daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli a biranen Tehran, Qom da Mashhad, inda za a binne shi a ranar 9 ga watan Yuli.
Rahotanni sun ce duk da rashin halartar jana’izar, Mojtaba Khamenei zai ci gaba da jagorantar harkokin ƙasar tare da sa ido kan shirye-shiryen makokin ƙasa daga wani wuri da jami’an tsaro suka tanada.