Najeriya ta zama ƙasa ta farko a nahiyar Afirka a fannin ƙarfin tattalin arziki, kamar yadda rahoton World Competitiveness Ranking 2026 na (IMD) ya bayyana.
Rahoton ya tantance ƙasashe 70 na duniya bisa manyan fannoni huɗu da suka haɗa da ƙarfin tattalin arziki, ingancin gwamnati, yanayin gudanar da kasuwanci da kuma ababen more rayuwa.
A cewar rahoton, Najeriya ta samu maki 45.2 a fannin ƙarfin tattalin arziki, inda ta kasance ta 55 a duniya, tare da zarce dukkan ƙasashen Afirka da aka haɗa a rahoton.
Bayan Najeriya, Afirka ta Kudu ce ta zo ta biyu a nahiyar da maki 36.27, sai Ghana da 34.6, Kenya da 33.19, Namibia da 22.3, sannan Botswana da 18.25.
Sai dai duk da wannan nasara, Najeriya ta sauka daga matsayi na 67 zuwa na 68 cikin ƙasashe 70 a jerin ƙasashe mafi ƙwarewa a duniya, inda ta samu maki 38.8.
Rahoton ya danganta wannan koma baya da matsalolin da suka shafi ababen more rayuwa, ingancin gwamnati da kuma yanayin gudanar da harkokin kasuwanci.