Fadar Shugaban Najeriya ta bayyana cewa babu gaskiya a zarge-zargen da aka yi wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, na karɓar cin hanci.
Zargin ya fito ne daga Yarima Adeniyi Adeyemi, wanda ya ce shi ne Darakta Janar na Presidential Foreign Intervention Promotion Council/Presidential Economic Advisory Council.
Ya yi ikirarin cewa an nemi ya biya kuɗin tallafin fara aiki da ya haura naira biliyan 27 domin a amince da hukumar.
Haka kuma, Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da karɓar Naira miliyan 400 daga wani mutum domin tabbatar masa da mukamin shugaban hukumar, tare da cewa har yanzu ana bin saura Naira miliyan 200.
Sai dai Femi Gbajabiamila ya musanta dukkan zarge-zargen, yayin da Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba su da tushe.