Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn gurfanar da ɗalibai mata takwas kan gobarar da ta hallaka ɗalibai...

An gurfanar da ɗalibai mata takwas kan gobarar da ta hallaka ɗalibai 16 a Kenya

Wata babbar kotu a Kenya ta gurfanar da ɗalibai mata takwas bisa zargin hannu a gobarar da ta tashi a ɗakin kwanan dalibai, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗalibai 16 tare da jikkata wasu 79.

Lamarin ya faru ne a ƙarshen watan Mayu a makarantar Utumishi Girls’ Academy Senior School da ke garin Gilgil, a gundumar Nakuru.

Yawancin ɗaliban makarantar na tsakanin shekaru 15 zuwa 18 ne.

Waɗanda ake tuhuma sun bayyana a gaban Alkaliya Diana Kavedza a Babbar Kotun Kibera da ke Nairobi, inda suka musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Har yanzu dai masu gabatar da ƙara ba su bayyana ƙarin bayanai kan shari’ar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments