Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHisbah ta cafke almajirai uku kan zargin amfani da miyagun ƙwayoyi a...

Hisbah ta cafke almajirai uku kan zargin amfani da miyagun ƙwayoyi a Kebbi

Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta kama wasu almajirai uku da ake zargi da amfani da miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na jihar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata, 30 ga Yuni, 2026, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna yaran masu shekaru 13, 11 da 10 sun fito ne daga Jihar Neja, Ƙaramar Hukumar Maiyama da kuma Birnin Kebbi.

Hisbah ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike domin gano yadda yaran suka shiga wannan dabi’a, tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa sakamakon binciken.

Hukumar ta kuma yi kira ga iyaye, malamai da sauran al’umma da su ƙara sa ido kan tarbiyyar yara, tare da gaggauta sanar da hukuma idan sun lura da duk wani abu da ka iya jefa yara cikin miyagun dabi’u.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments