Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta bayyana gamsuwarta da shirye-shiryen da Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Tsafe (FUHST) da ke Jihar Zamfara ta yi gabanin fara karatun ta.
A yayin aikin tantance kayan aiki da shirye-shiryen jami’ar, jami’an NUC sun duba ko an cika dukkan ƙa’idojin da suka haɗa da malamai ƙwararru, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu na zamani (e-Library), da sauran muhimman kayayyakin koyarwa.
Tawagar tantancewar ta ziyarci shirye-shiryen karatu da suka haɗa da Likitanci (MBBS), Likitan Haƙora (BDS), Pharmacy (Pharm.D), Occupational Therapy, Biotechnology, Artificial Intelligence da sauran fannonin da suka shafi kimiyyar lafiya.
Shugaban tawagar tantancewar na fannin Likitanci da Likitan Haƙora, Farfesa Muhammad Manga, ya yaba da irin kayan aikin ilimi da jami’ar ta samar. Haka kuma, Dr. Umar Farouk Abubakar daga tawagar tantance fannin Pharmacy ya ce tsarin karatun jami’ar ya dace da ƙa’idojin NUC, tare da yabawa ingancin kayan koyarwar da aka tanada.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya gode wa jami’an NUC bisa tantancewar da suka gudanar, yana mai tabbatar da cewa jami’ar za ta gyara duk wasu abubuwan da aka ba ta shawarar ingantawa kafin fara karatu.