Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da ƙoƙarin Shugaba Donald Trump na soke haƙƙin zama ɗan ƙasar Amurka ga jariran da aka haifa a cikin ƙasar.
Kotun ta tabbatar da cewa wannan haƙƙi yana da kariya a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar.
Alƙalai shida ne suka goyi bayan hukuncin, yayin da uku suka nuna rashin amincewa.
Bayan hukuncin, Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa, yana mai cewa abin takaici ne, sai dai ya ƙara da cewa Majalisar Dokokin Amurka na da ikon yin doka kan batun.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam sun yaba da matakin kotun, suna mai cewa hukuncin ya kare wani muhimmin haƙƙi da kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada.