Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani wurin haƙar ma’adinai da ke Nyango a gundumar Gyel, Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu biyu.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:50 na safiyar ranar Talata, yayin da ma’aikatan haƙar ma’adinai ke gudanar da aikinsu. Lamarin ya jefa ma’aikata da mazauna yankin cikin firgici, inda da dama suka tsere domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin, Chuwang Rogo, ya ce maharan sun kutsa cikin wurin haƙar ma’adinan tare da buɗe wuta kan ma’aikatan kafin su tsere.
Ƙungiyar matasan Berom (Berom Youth Moulders Association – BYM) ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa hakan na nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin Gyel da al’ummomin da ke maƙwabtaka da shi.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Rwang Tengwong, ya ce ba wannan ne karo na farko da ake kai irin wannan hari ba, yana mai cewa mazauna yankin sun daɗe suna ƙorafin hare-haren da ake kai musu.
Ƙungiyar ta buƙaci jami’an tsaro da gwamnati su rushe maboyar masu laifi tare da ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen hare-haren da ake yawan kai wa yankin.
Sai dai ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen Jihar Filato ta musanta zargin da BYM ta yi cewa wasu Fulani ne suka kai harin, tana mai cewa zargin ba gaskiya ba ne.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.