Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya za ta nemi diyya kan dukiyoyin ’yan ƙasarta da suka bari...

Najeriya za ta nemi diyya kan dukiyoyin ’yan ƙasarta da suka bari a Afirka ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta tuntubi gwamnatin Afirka ta Kudu domin neman a biya diyya kan dukiyoyin da ’yan Najeriya da suka bari a ƙasar bayan dawowarsu gida sakamakon hare-haren nuna kyamar baƙi.

Muƙaddashin Babban Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Alexander Ajayi, ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Channels Television, inda ya ce gwamnati ta fara tattara bayanai kan kadarorin da ’yan ƙasar suka bari domin amfani da su wajen tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu.

A cewarsa, an umarci dukkan ’yan Najeriya da aka dawo da su su gabatar da cikakken bayani kan kadarorinsu, ciki har da gidaje, kasuwanci, motoci da sauran dukiyoyi, domin gwamnati ta yi ƙoƙarin tabbatar da an kare haƙƙinsu.

Ya jaddada cewa shirin gwamnatin bai takaita ga kwaso ’yan ƙasar zuwa gida kaɗai ba, har ma ya haɗa da ƙoƙarin tabbatar da an samu diyya kan asarar da suka yi sakamakon rikicin.

A wani ɓangaren kuma, wasu ƙarin ’yan Najeriya 271 sun isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas bayan an kwaso su daga Afirka ta Kudu. Wasu daga cikinsu sun bayyana halin da suka fuskanta, tare da gargaɗin sauran ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan game da tafiya zuwa ƙasar saboda ƙaruwar hare-haren nuna kyamar baƙi.

Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu ‘yan Afirka ta Kudu suka gudanar, bayan wa’adin da aka bai wa baƙin da ba su da takardun zama na halal ya cika, abin da ya ƙara tayar da hankali tare da haifar da fargaba tsakanin ’yan kasashen waje da ke zaune a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments