Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen Dala biliyan 1.25 domin tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa zuba jari, ƙarfafa harkokin kasuwanci da kuma inganta tattalin arziƙin ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar a ranar Laraba, inda ya kuma ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.
A cewar Bankin, sabon shirin haɗin gwiwar zai mayar da hankali ne kan tallafa wa sauye-sauyen tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, bunƙasa jarin masu zaman kansu da kuma inganta rayuwar al’umma.
Ana sa ran sabon bashin zai taimaka wajen aiwatar da muhimman tsare-tsaren ci gaba da gwamnatin Najeriya ke yi, tare da ƙarfafa yanayin kasuwanci da jawo ƙarin masu zuba jari cikin ƙasar.
Najeriya na ci gaba da karɓar tallafin Bankin Duniya domin aiwatar da ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban, yayin da gwamnatin ƙasar ke fuskantar ƙalubalen bunƙasa tattalin arziƙi da rage talauci.