Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da shirin kafa cibiyoyin koyon ilimin zamani na guda 13 (Digital Learning Centres) a wasu zaɓaɓɓun makarantu domin inganta amfani da fasaha wajen koyarwa da koyo.
Shugabar Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Benue (SUBEB), Grace Adagba, ce ta bayyana hakan a wani taron da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da Hukumar UBEC suka shirya a Abuja kan amfani da kayan aikin zamani a fannin ilimi.
A cewarta, cibiyoyin za su samar da yanayin koyo na zamani da zai taimaka wajen inganta koyarwa, ƙara wa ɗalibai damar samun ingantattun kayan karatu da kuma bunƙasa ilimin fasaha a makarantu.
Ta bayyana cewa shirin ya yi daidai da manufar Gwamna Hyacinth Alia na sauya fasalin ilimi ta hanyar amfani da fasahar zamani. Ta kuma jaddada aniyar SUBEB na aiwatar da sabbin dabarun koyarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da UBEC ke gabatarwa.
Adagba ta ƙara da cewa haɗa fasaha cikin tsarin koyarwa zai bai wa ɗalibai ƙwarewar da za ta ba su damar gogayya a duniyar da ke ƙara dogaro da fasahar zamani.