Iyalan Abdullahi Bello, wani matashi da aka kashe a yankin Rantiya da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, sun buƙaci a yi musu adalci, suna zargin cewa an kashe shi ne bayan wasu sun yi masa kuskuren ɗaukarsa Bafullatani.
’Yar uwarsa, Hannatu Bello, ta shaida wa Daily Trust cewa Abdullahi ya bar gida a ranar Lahadi amma bai dawo ba. Daga baya ne ’yan sanda suka kira iyalansu suka sanar da su cewa an same shi a sume bayan wasu fusatattun mutane sun kai masa hari.
Ta ce ita da mahaifiyarsu sun garzaya Babban Asibitin Dadin Kowa, inda suka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Sai dai daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.
A cewarta, jami’in binciken lamarin ya gaya musu cewa wasu jami’an ’yan sanda da ke sintiri sun samu rahoto daga jami’an tsaro na sa-kai cewa wasu mutane sun doke Abdullahi bayan sun yi zargin cewa Bafullatani ne.
Hannatu ta ce gawar ɗan’uwanta na ɗauke da raunukan sara da kuma alamun an shake shi, yayin da jini ke fita daga bakinsa. Ta jaddada cewa ɗan’uwanta ba Bafullatani ba ne, kuma ta buƙaci rundunar ’yan sandan Jihar Filato ta gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk masu hannu a kisan.
Ta kuma roƙi jami’an bincike su binciki wayar marigayin da ke hannun ’yan sanda domin gano mutumin da ya yi magana da shi na ƙarshe kafin aukuwar lamarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.